A yayin bikin, ministan kula da harkokin cikin gida na Aljeriya Nouredine Bedoui ya ce, yanzu ana fuskantar kalubale da barazana da dama a nahiyar, ciki har da aikata laifukan ta'addanci, da fasa kwaurin makamai da kwayoyi, da safarar mutane, kuma ya zama dole a inganta hadin gwiwa a tsakanin kasashen Afirka kan aikin tsaro da harkokin 'yan sanda don yaki da dukkan nau'o'in laifuffukan. Ya lura da cewa, kafa kungiyar Afripol yana da muhimmanci game da daidaita matakan da 'yan sanda na kasashen Afrika suka dauka, musamman ma a fannin yaki da laifukan ta'addanci da fasa kwaurin kwayoyi.
Shugaban 'yan sanda na Aljeriya Abdelghani Hamel ya ce, kungiyar Afripol ta kasance wani muhimmin kashi ne na tsarin hadin gwiwar 'yan sanda na kasashen duniya, wadda ta kuma kasance wani babban jigo ne wajen tabbatar da zaman lafiya a duniya.(Bako)