Amma duk da wanna matsala, ma'aikatar harkokin wajen Aljeriya ta yi tsaya imanin cewa, 'yan kasar Libiya dake gaba da juna za su iya fuskantar kalubalen tsaro da kuma kai ga kiyaye zaman jituwa na 'yan kasar, fadin kasar Libiya, da 'yancin kasar Libiya da kuma hada kan al'ummomin Libiya baki daya.
Bisa wannan manufa, Aljeriya ta jaddada niyyarta na yin aiki tare da dukkan bangarorin Libiya, da ma kungiyoyin ta'addanci da MDD ta amince da su cikin shirin warware rikicin da kasar take fama da shi tun yau da kusan shekaru hudu.
Tun a ranar Talata, ake bata kashi tsakanin kungiyar IS da ke Libiya da mayakan sa kai na cikin gida domin kwace ikon birnin Syrte.
A cewar kamfanin dillancin labaran Libiya na LANA, kungiyar IS da ke Libiya ta fille kan wasu mayakan goma sha biyu da ke adawa da ita, kuma ta rataye su lokacin da ake gumurzun kwace birnin Syrte. (Maman ADA)