in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Akwai yiwuwar hauhawar kudin ruwa inji jami'in asusun ajiyar Amurka
2016-01-07 10:36:46 cri
Mataimakin shugaban asusun ajiya na kasar Amurka Stanley Fischer, ya ce mai yiwuwa ne a kara yawan kudin ruwa, sama da yadda masu hada-hadar kudade ke tsammani a bana.

Fischer wanda ya yi wannan tsokaci yayin tattaunawar sa da kafar talabijin ta CNBC, ya kara da cewa sashen zartaswa na hasashen yiwuwar kara kudin ruwa har karo 4 a wannan shekara, duk da cewa kasuwannin hada-hadar kudaden na hasashen kari sau biyu ne rak.

Kalaman jami'in asusun ajiyar kasar ta Amurka na zuwa ne makwanni uku, bayan da babban bankin kasar ya daga matsayin kudin ruwa na rancen da ake samarwa bisa matsakaicin zango, a karon farko cikin kusan karni guda.

Wasu jami'an gwamnatin Amurkan dai na dari-dari da wannan mataki na mahukuntan kasar, game da daga matsayin kudin ruwa da a kalla maki 25 daga sifili, matakin da ake ganin na iya rage karuwar farashin kayayyaki, wanda kuma ka iya shafar tattalin arzikin kasar baki daya.

Wata takardar bayanan ayyukan hukuma da aka fitar a ranar Laraba, mai kunshe da manufofin da gwamnatin tarayyar Amurkar ta amince da su, a zaman ta na 15 da 16 ga watan Disambar da ya shude, ta hakaiton Fischer na bayyana hasashen kara raguwar hauhawar farashin kayayyaki, zuwa mizanin da babban bankin kasar ya amince da shi na kaso 2 ciki dari, a daidai gabar da farashin mai da kuma darajar kudin kasar ke kara daidaita.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China