Rahotanni na cewa an gama aiki a wurare 6 cikin wadannan yankuna biyu, wadanda suka hada da filin wasan kwallon hannu, da na goal ball, da babban dandalin watsa labarai, da kuma filin kwallon golf. Sauran su ne filin wasan tseren Babura da na tseren kwale-kwale.
Bisa jimilla, "Olympic Park" zai karbi bakuncin wasannin Olympic 16, da kuma na nakasassu 9. Bangaren wasannin ruwa shi ma a cewar masu lura da aikin ya kusa kammala, yayin da kuma na kwallon tennis ya kai kimanin kaso 90% na kammala.
A yankin Deodoro kuwa, aikin filayen wasan kwallon hockey ya kai ga kaso 99%, yayin da aikin filin "Youth Arena" ya kai kusan kaso 75%. Bisa tsarin aikin, yankin Deodoro zai karbi bakuncin wasannin Olympic 22 da kuma na gasar nakasassu 4.(Saminu Alhassan)