in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yanayin da kasar Brazil ta ke ciki ba zai yi tasiri ga gasar wasannin Olympics da za a gudanar a birnin Rio ba
2015-09-25 16:32:32 cri

Yanayin da kasar Brazil ta ke ciki ba zai yi tasiri ga gasar wasannin Olympics da za a gudanar a birnin Rio ba

Tun a wannan shekarar ce, yanayin tattalin arzikin kasar Brazil ya ci gaba da tsananta, lamarin da ya haifar da zanga-zangar nuna adawa da gwamnatin kasar. Amma shugaban kwamitin shirya gasar wasannin Olympics na Rio de Janeiro Carlos Arthur Nuzman ya bayyana a kwanakin baya cewa, yanayin da kasar Brazil ta ke ciki ba zai yi tasiri ga gasar wasannin Olympics da za a gudanar a birnin Rio ba.

Nuzman ya bayyanawa 'yan jarida a birnin Fortaleza dake arewa maso gabashin kasar Brazil cewa, a na ci gaba da shirye-shiryen gudanar da gasar wasannin Olympics yadda ya kamata. A ganinsa, ba a samu wata matsala a yayin da ake shirya gasar cin kofin duniya a shekarar bara a kasar Brazil ba, kuma za a gudanar da dukkan shirye-shiryen gudanar da gasar wasannin Olympics a karkashin jagorancinsa yadda ya kamata.

Bugu da kari, yanayin tattalin arzikin kasar ta Brazil haifar da koma-baya. Kana ana zargin kamfanin samar da man fetur mallakar gwamnatin kasar Brazil da laifin cin hanci, wanda hakan ya shafi wasu kamfanonin da suke gudanar da ayyukan gine-ginen wasannin Olympics. Amma Nuzman ya bayyana cewa, wannan ba zai kawo illa ga gudanar da gasar wasannin Olympics din ba, domin komai na tafiya kamar yadda ya kamata.

IOC ya sanar da sunayen birane 5 da suke neman iznin daukar bakuncin gasar wasannin Olympics ta shekarar 2024

Kwamitin shirya gasar wasannin Olympics na duniya wato IOC ya sanar a birnin Lausanne dake kasar Switzerland a kwanakin baya cewa, birane 5 wato Budapest, Hamburg, Los Angeles, Paris da kuma Rome za su shiga takarar neman daukar bakuncin shirya gasar wasannin Olympics ta shekarar 2024.

Bisa bukatun kwamitin IOC,ana bukatar biranen da suke son shiga takarar da su mika takardun bukatunsu kafin ranar 16 ga wannan wata. Tuni dai wadannan birane 5 suka yi haka, kuma shugaban kwamitin IOC Thomas Bach ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa, kwamitin na maraba da takardun da wadannan biranen 5 da suke neman samun iznin daukar bakuncin gasar wasannin Olympics suka gabatar mata.

Thomas Bach ya kara da cewa, bisa tsarin kwamitin IOC, biranen da suke neman iznin daukar bakuncin gasar wasannin Olympics ta shekarar 2020 za su bayyana a gaban kwamitocin IOC don bayyana musu irin shirye-shiryen da suka yi game da daukar bakuncin gasar.

A bisa alkawarin da ya yi na zabar biranin da zai dauki bakuncin gasar wasannin Olympics cikin gaskiya da adalci, kwamitin IOC ya gabatar da wasu ka'idojin da kasa ya kamata ta cika game da neman iznin daukar bakuncin gasar wasannin Olympics da farko. Ban da wannan kuma, kwamitin IOC ya bayyana cewa, zai samar da taimakon kudin da yawansu ya kai dala biliyan 1.7 da kuma bada hidima ga biranen 5.

Za a jefa kuri'u don zaben birnin da zai dauki bakuncin gasar wasannin Olympics ta shekarar 2024 yayin cikakken zama na 130 na kwamitin IOC da za a gudanar da a birnin Lima dake kasar Peru a shekarar 2017.(Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China