Ministan harkokin wajen Brazil Mauro Vieira da takwaransa Laurent Fabius na Faransa, sun tabbatar da hakan ne a yayin wani taro kan sha'anin tsaro da suka gudanar a birninin Brasilia a karshen wananan mako.
Da yake jawabi a taron manena labarai, Mista Vieira ya ce, dama dai Fabius ne ya gabatar da bukatar neman a gudanar da tattaunawar, wanda ya ce tuni batun ya samu karbuwa daga bangaren gwamnatin Brazil.
Wannan sanarwa ta zo ne kwanaki 9 bayan wasu jerin hare hare a birnin Paris wanda yayi sanadiyyar lakume rayukan mutane sama da 100, kuma kasar ce ake saran zata karbi bakuncin taron MDD kan batun sauyin yanayi, tsakanin ranakun 30 ga wannan wata zuwa 11 ga watan Disambar wannan shekara.
Ya kara da cewar, a tarihi, kasar Brazil bata da makiya, sai dai duk da hakan, ya bukaci kasashen duniya da su bullo da dabarun yaki da ta'addanci, a cewar sa hare haren zasu iya fadawa kan kowace kasa a duniya.
Wasnnin Olympics na Rio na shekarara ta 2016, wanda za'a gudanar daga ranar 5 zuwa 21 ga watan Augusta na shekarar badi, ya kasance na farko da kasar wacce ke kudancin Amurka zata karbi bakuncin sa.(Ahmad Fagam)