in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tawagar walikan Beijing masu neman daukar bakuncin wasannin Olympics na lokacin sanyi na shekarar 2020 ta isa birnin Kuala Lumpur
2015-07-30 09:52:41 cri
Tawagar wakilan Beijing masu neman daukar bakuncin wasannin Olympics na lokacin sanyi na shekarar 2020, ta isa birnin Kuala Lumpur dake kasar Malaysia a ranar Asabar da yamma. Ana fatan jami'an tawagar za su halarci cikakken zama na 128, na kwamitin wasannin Olympics na duniya wato IOC.

Za a gudanar da zaman ne tsakanin ranekun 31 ga watan Yuli zuwa 3 ga watan Agustar dake tafe, inda za a sanar da sakamakon zaben birnin da zai dauki bakuncin gasar wasannin Olympics na lokacin sanyi na shekarar 2020.

Shugaban kwamitin neman daukar bakuncin gasar, kuma magajin birnin Beijing Wang Anshun ya bayyana cewa, tawagar wakilan Beijing masu neman daukar bakuncin gasar za ta aiwatar da wasu ayyukansu, da shaidawa duniya burin jama'ar Sin, da begen su ga wasannin Olympics, da kuma imanin da suke da shi ga karfin birnin Bejing na daukar bakuncin gasar.

A ranar 31 ga watan Yuli wadda za ta kasance ranar zaben biranen dake neman daukar bakuncin gasar wasannin na Olympics, biranen Almaty da birnin Beijing za su gabatar da bayanai, da amsa tambayoyi ga membobin kwamitin IOC. Daga baya kuma biranen biyu za su gudanar da taron manema labaru. Da yammacin wannan rana kuma, bayan da aka saurari rahoton kwamitin bincike na IOC, membobin IOC za su jefa kuri'u, na zabar birnin da zai dauki bakuncin gasar wasannin Olympics na lokacin sanyi na shekarar 2020. Bayan zaben kuma, kwamitin IOC zai gudanar da biki na musamman, inda a lokacin ne shugaban kwamitin IOC Thomas Bach zai sanar da sunan birnin, sa'an nan a sanya hannu kan yarjejeniyar daukar bakuncin wasannin Olympics tare da birnin da ya lashe zaben. Daga karshe kuma shugaban na IOC da wakilan birnin za su gudanar da taron manema labaru tare. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China