Kamar farashin tikitin wasannin Olympics na Rio, farashin tikitin wasannin Olympics na nakasassu na Rio ba shi da tsada, inda farashin tikitin miliyan 2 cikin miliyan 3 da dubu 300 da za a sayar ba zai kai kudin Brazil Real 30 ba, kimanin dalar Amurka 7 ke nan. Shugaban kwamitin wasannin Olympics na nakasassu na duniya Philip Craven, yana fatan yawan tikitin da ake sayar a wannan karo zai zarce yawan wanda aka sayar a yayin wasannin Olympics na nakasassu na birnin London, wato miliyan 2 da dubu 700.
Za a gudanar da gasar wasannin Olympics ajin nakasassu na birnin Rio de Janeiro ne tsakanin ranekun 7 zuwa 16 ga watan Satumbar badi, inda 'yan wasa kimanin 4,350 daga kasashe da yankuna 178 za su halarci gasar.(Zainab)