Keitany wadda ta kuma zamo ta hudu a gasar Olympics a birnin London, gasar ta ta karshe kafin ta tafi hutun haihuwa na shekaru biyu, ta ce yanzu haka ta shirya tsaf domin tinkarar kalubalen da ke tafe a birnin Rio. 'yar wasan ta kuma kara da cewa, nasarar da take fatan samu a wannan karo, za ta zamo mai matukar muhimmanci gare ta, kasancewar sauran 'yan wasa daga kasar ta wato Kenya, su ma zasu yi duk mai yiwuwa don ganin sun lashe lambar zinari a gasar dake tafe.
A gasar birnin New York, Keitany ta kammala gudu cikin sa'oi 2:24:25, inda ta tserewa wacce ke biye da ita da minti daya da 'yan dakikoki.
Keitany mai shekaru 33 da haihuwa, na da kwarewa ta musamman a fagen tsere, ta kuma bayyana dalilan nasarar ta da suka hada da kwazo, da aiki tukuru, da basirar iya tsere da ta samu bayan tsahon lokaci.(Saminu Alhassan)