An shirya gasar wasannin Olympics bisa cikakken tsari in ji magajin birnin Rio
A 'yan kwanakin baya ne magajin birnin Rio de Janeiro Eduardo Paes, ya bayyanawa wani taron manema labaru cewa, an gudanar da ayyukan share fagen gudanar gasar wasannin Olympics ta shekarar 2016 bisa tsarin da ake da shi a kasa, kuma birnin Rio ta shirya tsaf wajen gudanar da gasar a shekara mai zuwa.
A gun taron manema labarun, 'yan jarida fiye da dari daya daga kasashen duniya sun halarci taron, kuma Paes da shugaban kwamitin shirya gasar wasannin Olympics ta Rio Carlos Arthur Nuzman, sun yi bayani game da ci gaban da aka samu kan ayyukan share fagen gasar wasannin na Olympics.
A baya dai kwamitin wasannin Olympics na duniya wato IOC, ya taba nuna damuwar sa ga ayyukan share fagen gasar ta Olympic na birnin Rio, amma a daya hannun Paes ya bayyanawa taron manema labarun cewa birnin Rion zai shaidawa duniya cewa, 'yan kasar Brazil na da ikon kammala dukkan ayyukan share fagen gasar cikin lokaci.
Game da matsalar ingancin ruwa a mashigin tekun Guanabara, wanda za a yi wasan tseren jiragen ruwa mai filafilai cikin sa a yayin gasar ta Olympics, Paes da Nuzman sun tabbatar da cewa, ruwan zai dace da manufar kare lafiyar 'yan wasan.
Brazil za ta zuba jarin dala miliyan 165, domin tabbatar da tsaro a yayin gasar wasannin Olympics ta Rio
Ma'aikatar tsaron kasar Brazil, ta sanar da cewa gwamnatin kasar za ta zuba jari har dalar Amurka miliyan 165, domin tabbatar da tsaro a yayin gasar wasannin na birnin Rio de Janeiro ta shekarar 2016.
An yi hasashen cewa 'yan wasa kimanin dubu 15 daga kasashe da yankuna 205 ne za su halarci kasar Brazil, bisa gasar ta Olympics, da wasannin Olympics na nakasassu. Kana manyan jami'ai kimanin dari daya daga kasa da kasa su ma za su halarci kasar ta Brazil. Wanda hakan ya sanya batun tsaro ya zama batu mafi muhimmanci.
Game da hakan, ma'aikatar tsaron kasar Brazil ta sanar da cewa, za a jibge sojoji dubu 20 a birnin Rio de Janeiro, da kuma wasu sojoji dubu 18 a wuraren da za a gudanar da gasannin, ciki hadda na kwallon kafa domin tabbatar da tsaro.
Ban da sojoji dubu 38, kasar Brazil za ta tattara 'yan sanda da sauran jami'an tsaro dubu 47. Adadin jimillar jami'an tsaro da za a jibge zai karu da ninka biyu bisa na gasar wasannin Olympics ta birnin London da ta gabata a shekarar 2012.(Zainab)