Madam Panza ta kara da cewa, kasar Afirka ta Tsakiya tana son ci gaba da habaka dangantakar zumunci dake tsakaninta da kasar Sin, haka kuma, tana fatan kasar Sin za ta ci gaba da taimakawa kasar Afirka ta Tsakiya wajen sake gina kasar, inda ta ce, batun tsaro shi ne abin ya fi damun gwamantin kasar.
An sha fuskantar tashin hankali a kasar Afirka ta Tsakiya, inda a ran 23 ga watan Yuli na wannan shekara, bangarorin biyu da rikicin kasar ya shafa da suka hada da kungiyar anti-Balaka da kuma kungiyar da ke adawa da tsohuwar gwamantin kasar ta Seleka suka sanya hannu kan wata yarjejeniyar dakatar da rikice-rikice a birnin Brazzaville, don fara shawarwarin sulhu a duk fadin kasar. (Maryam)