in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An fidda muhimman labarai guda 10 da suka faru a duniya a shekarar 2015
2015-12-30 11:30:37 cri
A yau Alhamis ne gidan Rediyon CRI da jaridar China Daily suka fidda manyan labaran guda 10 da suka faru a duniya a shekarar 2015 cikin hadin gwiwa.

Wadannan manyan labaran guda goma sun hada da, yadda kasar Sin ta tafiyar da harkokinta na diflomasiyya, ta ba da babbar gudummawa a kokarin gina sabuwar dangantakar kasa da kasa; da yadda kasar Sin ta fitar da takardar bayani game da shirin nan na zirin tattalin arziki na siliki da hanyar siliki ta ruwa na karni na 21, shirin da ya samu karbuwa daga kasashen dake kan hanyar siliki; da bayani game da yadda kungiyar IS ke ci gaba da kaddamar da hare-haren ta'addanci, lamarin da ya haddasa gasa tsakanin kasa da kasa tun bayan da kasar Rasha ta fara kadamar da hare-hare kan kungiyar; rahoto game da yadda aka kulla yarjejeniya a bankin zuba jari kan ayyukan more rayuwa na Asiya a birnin Beijing, wanda ya gaggauta kwaskwarimar tsarin sha'anin kudi a nan duniya; da batun kulla yarjejeniyar batun nukiliyar Iran bisa dukkan fannoni, duk da cewa, ana ci gaba da fuskantar wasu kalubaloli wajen warware batun gaba daya; akwai kuma rahoto game da yadda majalisar dokokin kasar Japan ta zartas da dokar tsaro, lamarin da ya haifar da damuwa ga kasashen da ke yankin gabashin Asiya da kewaye; sai kuma labari game da yadda masana suka gano wata duniya, bayan da suka tabbatar da cewa, akwai ruwa a duniyar Mars; sai kuma wani rahoton da ke bayani kan yadda kasashen duniya suka yi bukukuwan tuna da samun nasarar yakin duniya na biyu, inda kasashen Sin da Rasha suka jaddada bukatar kiyaye tsaron duniya; akwai kuma rahoto game da yadda matsalar 'yan gudun hijira ke ci gaba da haifar da kalubale a kasashen Turai, inda aka fara samun sabani a tsakanin mambobin kungiyar tarayyar kasashen Turai ta EU; daga karshe sai rahoto game da yarjejeniyar da aka cimma dangane da yadda za a magance matsalar sauyin yanayi bayan shekarar 2020 a yayin babban taron sauyin yanayi da aka gudanar a birnin Paris na kasar Faransa. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China