in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude dandalin taron tattaunawar raya Xinjiang na shekarar 2015 a Urumqi
2015-08-18 14:06:50 cri
A yau Talata 18 ga wata ne aka bude dandalin taron tattaunawar raya jihar Xinjiang ta kasar Sin a Urumqi babban birnin jihar, taron da ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin, da cibiyar nazarin ilmin zaman takewar al'umma na Sin, da kuma gwamnatin jihar Xinjiang mai cin gashin kan ta suka hada gwiwarsu wajen shiryawa.

Babban taken dandalin din shi ne, "kafuwar zirin tattalin arziki kan hanyar siliki babbar dama ce ga jihar Xinjiang a fannin neman bunkasuwa". Kana bisa taken taron, an tabbatar da batutuwa guda hudu da za a tattauna wadanda suka hada da, yadda za a iya gina cibiyar yankin hanyar siliki, da kuma kara mu'ammala da kasashe da yankunan dake kewayen yankin, da gudanar da ayyukan jihar mai cin gashin kanta yadda ya kamata, a matsayin babban tushen samun bunkasuwa da zaman karko a jihar, gami da hanyar da za a bi don fuskantar sabbin kalubaloli a yankin, musamman ma a fannin tsaro, da kuma gadon tarihi da al'adun hanyar siliki.

Cikin sakon taya murnar budewar dandalin wanda shugaban majalissar ba da shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar Sin Yu Zhengsheng ya aike ga mahalarta taron, ya ce a matsayin babbar jihar dake kan hanyar siliki, jihar Xinjiang tana da muhimmanci a yunkurin kasar Sin na bude kofa ga kasashen waje. A cewar jami'in, jihar tana da muhimmin matsayi a aikin sufurin hajoji tsakanin nahiyar Turai da Asiya, haka kuma cibiya ce ta al'adu da ba da ilmi tsakanin nahiyoyin biyu.

A daya bangaren ana fatan wakilan gida da ketare da suka halarci taron, za su iya tattaunawa cikin himma da kwazo, da kuma ba da shawarwari kan yadda za a iya karfafa musayar al'adu a tsakanin kasashe daban daban, ta yadda za a iya ciyar da hadin gwiwar kasashen gaba, da kuma tabbatar da ci gaban tattalin arziki da zaman lafiya a fadin duniya. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China