in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta yi kiran da a kara hada kai don yaki da ta'addanci
2015-12-22 20:33:50 cri

Kasar Sin ta yi kira ga kasashen duniya da su kara hada kai a yakin da ake yi da ayyukan ta'addanci, ta yadda za a kaucewa kura-kuren da ke faruwa kamar yadda sojojin kasar Turkiya suka harbo jirgin saman kasar Rasha a watan da ya gabata.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hong Lei wanda ya bayyana hakan a yau yayin taron manema labarai, ya tabbatar da cewa, kwararru daga kasar Sin tare da takwarorinsu na kasashen waje suna nazarin akwatin nadar bayanan jirgin bisa gayyatar kasar Rasha.

Mr Hong ya ce, kasar Sin ta lura da cewa, jirgin saman yakin na Rasha yana aikin yakar sansanonin 'yan ta'adda ne a kasar Syria kamar yadda gwamnatin Syria ta bukata. Yana mai cewa, harbo jirgin saman yakin na Rasha a wannan lokaci, wani babban koma baya ne ga kokarin da kasashen duniya ke yi na yaki da ayyukan ta'addanci.

Daga karshe Mr Hong ya yi kira ga dukkan bangarorin da abin ya shafa, da su kara hada kai a yakin da ake yi da ayyukan ta'addanci, tare da daukar kwararan matakai na hana aukuwar makamancin abin da ya faru da jirgin saman yakin kasar Rasha a Turkiya.

Bayan faruwar lamarin dai, kwamitin sulhu na MDD ya amince da wani kuduri da ke kira ga kasashe mambobin kwamitin, da su dauki dukkan matakan da suka dace na ganin an dakile aukuwar munanan ayyukan da kungiyar IS da sauran kungiyoyin 'yan ta'adda ke aikatawa a doron kasa.(Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China