in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta mai da martani game da kisan basine da kungiyar IS ta yi
2015-11-19 11:37:37 cri

A ranar 19 ga watan nan, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hong Lei ya yi bayani game da kisan wani Basine da kungiyar IS ta yi, inda a cewarsa, kungiyar IS ta yi garkuwa da wani Basine mai suna Fan Jinghui , kuma daga bisani ta hallaka shi. Kasar Sin ta nuna ta'aziyya game da wannan rashi, sannan ta jajantawa iyalin marigayin.

Hong Lei ya kara da cewa, bayan da aka yi garkuwa da Mr. Fan, gwamnatin Sin da jama'arta sun nuna masa damuwa sosai. Sin ta kafa shirin ko-ta-kwana tun da farko don kubutar da shi. Amma, kungiyar ta'addanci ba ta da gaskiya da tausayi, kuma ta aikata kisan rashin imani. Gwamnatin Sin ta yi Allan wadai da lamarin maras tausayi, kuma tabbas Sin za ta gurfana da masu laifi gaban kotu.

A cewar kakakin, ta'addanci ya zama abokin gaba na 'yan Adam baki daya. Kasar Sin na adawa da laifin ta'addanci, kuma za ta yi yaki da dukkan laifuffukan ta'addanci masara tausayi. A waje daya kuma, Sin za ta ci gaba da inganta hadin gwiwa da kasashen duniya wajen yaki da laifin ta'addanci, don tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China