Abdirahman Sandhere wanda aka fi sani da Ukash, an kashe shi ne lokacin da sojojin sama na Amurka suka kai hari a Somliya a ranar 2 ga wannan watan na Disamba, in ji kakakin Pentagon Peter Cook a cikin sanarwar da ya fitar.
Harin saman musamman daman aka kaddamar domin Sandhere, in ji Cook, yana mai bayanin cewa, akwai jami'ai biyu na rassan kungiyar ta al-Shabaab da harin ya rutsa da su har ila yau.
A wata sanarwa ta daban kuma da aka fitar a ranar ta Litinin, Peter Cook ya tabbatar da cewar, Abu Nabil, wanda aka fi sani da suna Wissam Najm Abd Zayd al Zubaydi, 'dan asalin kasar Iraqi da ya dade yana aiki tare da al-Qaida kuma babban jami'i a kungiyar IS dake Libya, shi ma an kashe shi a harin da aka kaddamar a ranar 13 ga watan Nuwamba.
Wannan shi ne karo na farko da Amurka ta kai harin saman a kan wani shugaban kungiyar ta IS a Libya, in ji Mr Cook.(Fatimah)