Kungiyar tattalin arziki da kudi ta yammacin Afrika (UEMOA) na neman sabbin hanyoyin samun kudade a karkashin wata gidauniya da aka ma taken "saukaka ma shiyyar samun hanya ta karko (FRAED)" domin kafa ayyukan samar da makamashi mai tsabta, tare da burin farko na cimma karfin wutar kantarki megwatts 200, in ji wata sanarwar kungiyar a ranar Talata a birnin Cotonou.
A cewar wannan sanarwa, da aka fitar bayan taron kwamitin manyan jami'ai kan sakamakon aiwatar da manyan ayyuka na shiyyar kan makamashi mai tsabta, da ya gudana a ranar Talata a birnin Cotonou, abin da aka shirya ba da wa ga gidauniyar FRAED shi ne Sefa biliyan 50 kwatankwacin dalar Amurka miliyan 100, wanda ya hada da taimakon kungiyar UEMOA da zai kai Sefa biliyan 10 kimanin kashi 20 cikin 100.
Haka kuma sanarwar ta bayyana cewa, asusun ci gaban makamashi (FDE) na aiki kuma taimakon da aka bayar ya kai Sefa biliyan 257 da miliyan 273, kwatankwacin fiye da dalar Amurka miliyan 514, daga ciki kasar Belgium ta ba da biliyan 7, 215. Wadannan kudade, a cewar sanarwar, za su taimaka wajen gudanar da manyan ayyuka 11 bisa jimillar kudi kimanin Sefa biliyan 200, domin warware matsalar karancin wutar lantarki a shiyyar kungiyar UEMOA. (Maman Ada)