Babban jami'in ofishin shirin MDD mai lakabin "kowa na amfani da makamashin bola-jari" dake birnin New York Takada Minoru, ya bayyana cewa kasar Sin, ta zama abin koyi a fannin raya makamashi na bola-jari a duniya, kuma mahukuntan kasar na daukar matakai masu inganci wajen kafa tsari na tsimin makamashi.
Mr. Takada Minoru ya kuma bayyana fatan kasar Sin za ta ingiza hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa, da kuma tsakanin kasashe masu ci gaba da masu tasowa, domin taimakawa kasashen Asiya da Afrika, wajen daidaita batun makamashi, da kara taka rawa mai yakini kan cimma burin amfana daga makamashi a duniya.
Babban magatakardan MDD Ban Ki-Moon ne ya gabatar da shirin "kowa na amfani da makamashi na bola-jari" a shekarar 2011, wanda ya samu martani daga kasashe fiye da 100, ciki har da kasashe masu tasowa 85.
A matakin farko na gudanar wannan shiri, an tsara ajanda tare da kasashe 30, ciki har da kasashen Uganda da Ruwanda, domin taimaka musu wajen cimma burin raya makamashi, ta hanyar samar musu da fasahohi, da jari, da kuma tsara musu manufar kasuwanci da ta dace.(Lami)