Eduardo del Buey wanda shi ne mataimakain mai magana da yawun magatakardan MDD Ban Ki-Moon, ya ce Brahimi zai zo ranar Jumma'a 19 ga watan nan don yin jawabi ga kwamitin tsaron MDD dangane da batun kasar Syria.
Ya ci gaba da cewa Brahimi zai yi jawabin ne bayan manyan jami'an MDD da dama sun gabatar da nasu rahoto kan yanayin jin kan bil Adama a kasar.
Har yanzu dai ba'a cimma wata matsaya daya ba kan batun rikicin Syria wanda yanzu ya kai shekaru biyu duk da kokari da Brahimi yake yi tun lokacin da ya fara aikinsa a watan Agustan bara domin a samu cimma wata matsaya tsakanin gwamnatin kasar da 'yan adawa.
A yanzu haka aikin masu binciken zargin amfani da makamai masu guba, wanda gwamnatin ta Syria ta bukaci a gudanar ya tsaya cik saboda gwamntain kasar ta hana masu binciken su yi aikin a wajen Aleppo.
A ranar Litinin ne ma'aikatar harkokin wajen kasar Syria ta bayyana cewa bukatar MDD na yin cikakken bincike kan amfani da makamai masu guba a dukkan yankunan kasar Syria ya sabawa bukatar gwamnatin Syria.
A fadin del Buey, magatakardan MDD Ban Ki-Moon bayan wata ganawa da ya yi da shugaban kasar Amurka Barack Obama dangane da yiwuwar amfani da makamai masu guba a Syria, ya ce abin bakin ciki ne ganin cewa gwamnatin Syria ta ki amincewa da wannan bukata. (Lami Ali)