A ranar Alhamis 12 ga wata, kungiyar musamman ta MDD dake kasar Sudan ta Kudu wato UNMISS ta ba da lambar yabo ga sojojin kasar Sin 700 wadanda aka tura su karo na farko domin kiyaye zaman lafiya a kasar, sakamakon babbar gudummawar da suka bayar a cikin aikin wanzar zaman lafiya.
Ellen Margrethe Loj, wakiliyar musamman ta babban sakataren MDD kuma shugabar kungiyar UNMISS a cikin jawabin da ta gabatar a yayin bikin, ta nuna amincewa da kwarewar aiki da kuma da'ar da sojojin suka nuna yayin da suke gudanar da ayyuka iri daban daban.
Ta kuma lura da cewa, tun bayan da kasar Sin ta jibge sojojinta na wanzar da zaman lafiya a kasar Sudan ta Kudu, wadannan sojoji sun burge kungiyar UNMISS sosai, wadanda suka bayar da babbar gudummawa ga sha'anin shimfida zaman lafiya a kasar. (Kande Gao)