in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta yi maraba da a cimma yarjejeniya tsakanin bangarori biyu na Sudan ta kudu
2015-11-05 13:49:02 cri
Kungiyar tarayyar kasashen Afrika AU ta yi maraba da yarjejeniyar da aka cimmawa akan yadda za'a gudanar da yarjejeniyar zaman lafiyar da aka cimma a kasar Sudan ta kudu.

Gwamantin kasar Sudan ta kudu da kungiyar SPLM na sojojin dake adawa, da shugabannin SPLM da aka taba tsarewa a ranar Talata suka rattaba hannu a kan yarjejeniyar a birnin Addis ababa na kasar Habasha.

Nkosazana Dlamini-Zuma shugaban kwamitin kungiyar ta yi maraba da wannan yarjejeniyar da bangarorin uku suka cimma musamman game da aiwatar da tsarin tsaro wajen warware rikicin a kasar.

A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Laraba, an ce bangarorin sun kuma amince da daukan 'yan sanda na hadin gwiwwa don tabbatar da tsaron birnin na Juba da sauran garuruwa da suka hada da Bor, Malakal da kuma Bentui.

Kungiyar raya gwamnatocin kasashen gabashin Afrika ta IGAD ta dade tana shiga tsakani a wajen samar da zaman lafiya tun lokacin da rikicin ya barke a jaririyar kasar a duniya.

Shugaban kwamtin na AU ta yaba ma ma'aikatan tawagar IGAD da suka hada da Jakada Seyoum Mesfin, Janar Lazaro Sumbeiywo da Janar Mohammed El-dabi bisa ga kokarin su na taimaka ma masu ruwa da tsaki a kasar cimma zaman lafiya mai dorewa, a cewar sanarwar.

Haka kuma shugabar kwamitin na AU har ila yau tana zura ido don ganin an aiwatar da wannan yarjejeniya sau da kafa kamar yadda masu ruwa da tsakin kasar suka yi alkawari, hakan dai za a iya samar da muhalli mai kyau na kafa gwamnatin wucin gadi na hadaka. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China