in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin na kokarin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da kuma adalci a yankin Asiya da tekun Pacific da ma duniya baki daya
2015-11-10 19:22:43 cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hong Lei ya bayyana yau Talata cewa, kasar Sin kasa ce da ke tsayawa kan kiyaye tsari da dokokin kasa da kasa, kana tana bayar da gudummawarta a wannan fanni, baya ga yadda take kokarin kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali da adalci a yankin Asiya da tekun Pacific da ma duniya baki daya.

Hong Lei ya fadi haka ne yayin da yake mayar da martani kan kalaman da sakataren tsaron kasar Amurka Ashton Carter ya yi a kwanan baya, inda ya ce, an tabbatar da dokokin kasa da kasa da ake bi yanzu ne bisa hadin kan gamayyar kasa da kasa a karkashin jagorancin Majalisar Dinkin Duniya, kamar yadda kundin tsarin MDD ya tanada. Kana babbar ka'idar wadannan dokoki ita ce, bukatar kasashen duniya su girmama juna da kuma 'yancin kasa da yankunanta, da zaman daidai wa daida, da daina tsoma baki cikin harkokin cikin gidan juna. Ba wani dan kasar Amurka kawai yake da ikon tsara ko sauya oda da dokar kasa da kasa ba. (Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China