in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Yi ya halarci taron ministocin harkokin waje karo na uku na kungiyar goyon bayan Syria ta duniya
2015-12-19 11:56:29 cri

A jiya Jumma'a 18 ga wata, ministan harkokin waje na Sin Wang Yi ya halarci taron ministocin harkokin waje karo na uku na kungiyar goyon bayan Syria ta duniya a birnin New York, inda mista Wang ya bayyana ra'ayi da shawarar kasar Sin a fannoni 5.

Wadannan shawarwarin sun hada da kaddamar da shawarwari, tsagaita bude wuta, yin hadin gwiwa domin yaki da ta'addanci, sannan kuma da ba da taimakon jin kai, da kuma farfado da tattalin arziki.

A fannin kaddamar da shawarwari, Wang Yi ya ce kamata ya yi a yarda kowace jam'iyyar adawa su samu ikon shiga wannan shawarwarin, da zarar ba su aikata ayyukan ta'addanci ba, da nuna goyon baya ga daidaita matsaloli ta hanyar siyasa.

A fannin tsagaita bude wuta kuma ya ce kamata ya yi a yi la'akari bisa hakikanin yanayin da ake ciki, a sa kaimi a kai a kai. Mr Wang ya ce ya kamata kwamitin sulhu ya ba da izini cikin lokaci na kafa wani tsarin sa ido kan tsagaita bude wuta, kuma idan lokaci ya yi, zai jibge aikin kiyaye zaman lafiya a can.

Sannan a fannin yaki da ta'addanci kuma, ministan ya ce abin dake gaban kome shi ne kara samun daidaito, domin yin hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa.

Batun taimakon jin kai kuwa a ganin shi dole ne a gudanar da babban taron ba da taimakon jin kai na Syria yadda ya kamata, domin kara ba da agaji ga Syria da sauran kasashen dake kewayenta.

Sai kuma a fannin farfado da tattalin arziki, kamata ya yi a yi la'akari da kafa wani rukunin farfadowa na Syria, da kaddamar da babban taron kasashen taimakawa farfadowar Syria cikin lokaci.

Bayan haka, mista Wang ya furta cewa, daidaita matsalar Syria na da wuya sosai, shi ya sa kamata ya yi bangarori daban daban su yi hakuri da juna. Ana fatan za su yi amfani da wannan dama, su yi hadin gwiwa domin sa kaimi ga yunkurin daidaita matsalar ta hanyar siyasa. Sin za ta ci gaba da taka rawar a zo a gani kan wannan batu.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China