Gwamnan jihar Homs Talal Barazi ya fadawa kafofin yada labaru a wannan rana cewa, akwai dakarun adawa na Al-Nusra Front kimanin 274 da jama'arsu 450 da suka janye jiki zuwa jihar Idleb da ke yankin arewacin kasar. Ya ce sai dai za a kwashe makwanni da dama, yayin da suke janye jiki da daidaita takardunsu, daga bisani kuma, gwamnatin Siriya za ta sake gina yankin Wayir.
A ranar 1 ga watan nan ne, gwamnatin Siriya da bangaren adawa na kasar da ke birnin Homs suka daddale yarjejeniya, inda dakarun adawa na kasar kimanin 3000 za su janye jiki daga birnin Homs ko kuma mika wuya ga sojojin gwamnatin, sannan kuma za a saki wasu dakarun da aka tsare, abin da M.D.D.ta ce za ta sa ido game da wannan aiki.
Wadannan dakaru za su janye har zuwa jihar Idleb wato daya daga cikin cibiyoyin dakarun adawa na kasar.(Bako)