A cikin jawabin da ya yi a gaban manema labaru, Liu ya bayyana cewa, kasar Sin ta yi maraba da fadaden taron ministocin harkokin waje na kasashen dake shafar batun Syria da aka shirya a kwanan baya a Viena.
Liu ya kara da cewa, kwamitin sulhu ya riga ya zartas da kudurori da dama kan batun yaki da kungyiyoin 'yan ta'adda, ciki har da IS, an kuma samu ra'ayi bai daya a kai. Kasashe mambobin kwamitin, ciki har da Sin, da kuma kasashe masu halartar taron ministan harkokin waje na Viena dukkansu na goyon bayan yaki da kungiyar IS da sauran 'yan ta'adda bisa kudurin kwamitin sulhu. (Bilkisu)