Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Li Baodong, dake bayani a gaban manema labarai a ranar Asabar a birnin Vienna, inda yake halartat wani taron kasa da kasa kan rikicin Syria, ya bayyana cewa akwai bukatar a cimma tsagaita bude wuta baki daya a Syria, idan ana fatan gamayyar kasa da kasa ta yaki kowa ne irin ta'addanci cikin hadin gwiwa.
Taron kan ricikin Syria na gudana kwana daya bayan hare haren ta'addancin da suka abku a birnin Paris, wadanda suka yi sanadiyyar mutuwar mutane kimanin 129 da raunana 352.
Mataimakin ministan harkokin wajen Sin ya kuma bayyana ra'ayin cewa gyare gyaren da za'a yi domin wani rikon kwarya a Syria dole su yi dogaro kan sanarwar Geneva da kuma kasancewa a karkashin jagorancin MDD.
Mista Li Baodong yayi kira da a kara karfafa kokarin bada agajin kasa da kasa, tare da yin alkawarin cewa kasar Sin zata dauki matakai a wannan fanni. (Maman Ada)