Kakakin ya bayyana haka ne a yayin taron manema labarai da aka saba yi duk rana, ya kuma kara da cewa, Mr. Wang zai gabatar da shawarwarin da Sin take da su akan dakatar da bude wuta, cimma sulhu na siyasa, yaki da ta'addanci da kuma ayyukan da za'a gudanar bayan yaki.
Da yake bayyana goyon baya ga taron, Mr Hong Lei ya ce kasar ta Sin na fatan taron zai ingiza wani sulhuntawa a Syriyan sakamakon irin wannan ganawa har sau biyu a baya.
Bayan taron karo na uku na kungiyar, kwamitin tsaron MDD za ta kira taro a matakan ministoci duk a wannan ranar.(Fatimah)