Mr. Wang Min ya gabatar da wannan kira ne yayin da yake jawabi ga taron kwamitin sulhu game da batun fataucin mutane a yankunan dake fama da rikice-rikice. Ya ce a cikin 'yan shekarun da suka wuce, kungiyar IS da ta Boko Haram, da makamantan su, sun aikata laifukan kamawa da sayar da mutane a yankin Gabas ta Tsakiya da nahiyar Afirka da ma sauran wurare. Hakan a cewar sa ya haifar da babbar illa ga iko da moriyar mata da ta yara, tare da lalata yanayin zaman rayuwarsu.
A sabili da haka, Mr. Wang ya ce kamata ya yi kasashen duniya su yi hadin gwiwa tsakaninsu, domin ba da kariya ga iko da moriyar wannan rukuni na al'umma, a yankunan dake fama da rikice-rikice a duniya. (Fatima)