Kasar Sin na goyon bayan yin kwaskwarima ga kwamitin sulhu, a kokarin ganin ya kara sauke nauyin da aka dora masa bisa kundin tsarin MDD, tare da kara wakilcin kasashe maso tasowa, musamman ma kasashen Afirka, kamar yadda Hong Lei, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya shaidawa taron manema labarai a yau Talata
A jiya kamar yadda ya yi a baya, babban taron MDD karo na 69 ya tsai da kudurin dakatar da yin shawarwari tsakanin gwamnatoci dangane da batun yin kwaskwarima ga kwamitin sulhu, a babban taronsa karo na 70.
Dangane da lamarin, Hong Lei ya kara da cewa, ko da yake sassa daban daban ba su cimma daidaito kan batun yiwa kwamitin sulhu kwaskwarima ba, amma dukkansu na fatan kasashe mambobin kwamitin sulhu za su yi amfani da matsayinsu wajen jagorantar shawarwari ko tattaunawa kamar yadda doka ta tanada. (Tasallah Yuan)