in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da MDD za su shirya taron kolin mata na duniya
2015-09-17 20:48:06 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hong Lei ya shaidawa taron maname labarai a yau cewa, kasar Sin da hukumar kula da harkokin mata ta MDD za su shirya taron kolin mata na duniya,taron da yanzu haka aka tabbatar da cewa, shugabannin kasashe da kungiyoyin kasa da kasa kimanin 80 za su halarta.

Ya kuma kara da cewa, shekarar bana shekara ce ta cikon shekaru 20 da shirya taron kungiyar mata ta duniya da aka yi a nan Beijing, a shekarar 1995, tare da zartas da sanarwar Beijing da kuma manufofin kungiyar, matakan da suka taimaka ga ci gaban harkokin mata a duniya.

Haka kuma, Hong Lei ya ce, kasar Sin da hukumar kula da harkokin mata ta duniya sun shirya taron kolin ne domin sa kaimi ga shugabannin kasa da kasa da su gaggauta aiwatar da alkawarin da aka yi game da samar da daidaito a tsakanin maza da mata da kuma baiwa mata 'yanci, a wannan lokaci na cikon shekaru 20 da kafa kungiyar mata ta duniya a Beijing, inda shugabannin kasashen duniya za su taru a hedkwatar MDD. Bugu da kari, taron da shugabannin kasa da kasa za su yi game da batun mata yana da muhimminci matuka ga tarihin dan Adam. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China