Ana sa ran shugaban kasar Sin Xi Jinping zai halarci jerin manyan tarukan dangane da cika shekaru 70 da kafa MDD da za a yi daga ranar 26 zuwa 28 ga wata.
Wannan ne karo na farko da shugaba Xi ya halarci irin wannan taron koli na MDD.
A cikin bayanin, Sin ta bayyana ra'ayinta kan muhimman batutuwa dangane da cika shekaru 70 da kafa MDD daga dukkan fannoni, tare da bayyana matsayinta kan muhimmancin taron kolin, da amfanin kwamitin sulhu na MDD, da ayyukan kiyaye zaman lafiya da MDD ke gudanarwa, da harkokin kiwon lafiya da tsaro, batutuwan da suka shafi yara, da tarbiyya, da kare hakkin nakasassu, da batun sauyin yanayi, ayyukan ta'addanci, da tsaron yanar gizo ta internet, da hakkin bil'adam, da kara inganta ayyukan MDD da dai sauransu.(Fatima)