Mr. Gao ya bayyana hakan ne yayin da ake gudanar da taron ministoci karo na 10 na kungiyar cinikayya ta duniya wato WTO a kasar Kenya. Ya ce Sin na turawa kasashen Afrika kwararru da masana domin bada tallafi, tana kuma hadin gwiwa da kasashen nahiyar a fannoni da dama, ciki hadda fannin bunkasa masana'antu. Sauran sassan sun hada da aikin gona, da kawar da talauci, da kiwon lafiya da dai sauransu, musamman a fannin ba da jiyya, matakin da ya sami yabo matuka daga jami'ai da jama'ar kasashen na Afrika.
Idan ba a manta ba, shugaban kasar Sin Mista Xi Jinping ya gabatar da ra'ayinsa na "Manyan ginshikai biyar" da "Shirin hadin gwiwa a manyan fannoni goma" a taron koli na dandalin tattaunawar hadin kai tsakanin Sin da Afrika, wanda ya gabata a farkon wannan wata da muke ciki a birnin Johannesburg, inda kuma Mista Xi ya yi alkawarin samar da tallafin kudi har dala biliyan 60. Game da hakan, Mista Gao ya ce Sin ta samar da wadannan tallafi ne bayan wasu kasashe dake karbar tallafi sun yarda da samu goyi bayan manufofin, kuma za su shiga cikin wannan aiki.
Ya ce Hanyar da Sin da kasashen Afrika za su bi nan gaba dangane da hadin gwiwar su, za ta hanzarta bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin har ma dukkanin nahiyar Afrika baki daya. (Amina)