in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kaddamar da dandalin kiyaye muhalli tsakanin Sin da Afirka ta kudu
2015-11-18 19:46:16 cri

 

An kaddamar da dandalin kiyaye muhalli tsakanin matasa masu aikin sa kai na Sin da Afrika ta kudu, da kuma bikin baje kolin hotuna da aka dauka, na dabbobin daji tsakanin Sin da Afrika. An gudanar da wadannan taruka ne a jami'ar koyar da ilimin kimiyya ta Tshwane dake birnin Pretoria na Afrika ta kudu.

Dandalin da aka gudanar a wannan karo, na da zummar kira ga matasa da su kiyaye dabbobin daji dake daf da karewa, da kiyaye muhalli tare da bin tsarin sa. Kana da amfani da wannan zarafi mai kyau, wajen sa kaimi ga hadin gwiwa da mu'ammala tsakanin matasa masu aikin sa kai na kasashen biyu, ta yadda za su kara kwazo na daukar alhakin kiyaye muhalli a duniya.

Mataimakin shugaban hukumar kula da dazuzzuka a kasar ta Sin Mista Chen Fengxue, ya gabatar da jawabi a dandalin, inda ya bayyana cewa Sin da Afrika ta kudu, dukkansu na da dimbin dabbobin daji iri-iri, kuma suna daukar kare dabbobin daji da muhimmancin gaske.

Kaza lika kasashen na sanya himma wajen yaki da cinikin dabbobin dajin ba bisa ka'ida ba, hakan ne kuma ya sa kasashen biyu kara hada gwiwa a wannan fanni, musamman a fagen daukar matakan da suka wajaba, ciki hadda kiyaye muhalli, da kiyaye wanzuwar halittu iri-iri, da kulla wasu yarjeniyoyi na kiyaye fadama, da kiyaye dabbobin daji dake daf karewa, da hana yaduwar hamada da dai sauran su. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China