An bayyana wannan bukata ne yayin wani taron gabatar da rahoto game da samar da abinci mai gina jiki na bana wanda ya gudana a birnin Nairobin kasar Kenya. Mahalarta taron dai sun amince da bukatar samar da dama a siyasance ta rage tasirin wannan matsala, tare da fadada hanyoyin samar da abinci mai gina jiki ga al'ummar Afirka.
Da yake tsokaci yayin taron, babban sakatare a hukumar kula da kiwon lafiya na kasar Kenya Nicholas Muraguri, ya jinjinawa irin ci gaba da aka samu a wannan fanni, sai dai a daya bangaren ya bayyana bukatar hada karfi da karfe, wajen ganin an kawo karshen matsalar karancin abinci mai gina jiki kaco kan nan da shekara ta 2030.
Rahoton na bana dai ya bayyana irin nasarorin da aka cimma game da yunkurin da ake yi na dakile matsalar karancin abinci mai gina jiki a gabashin nahiyar Afirka, da ma daukacin nahiyar Afirka baki daya. Ya kuma yi karin haske game da sassan da ake fuskantar kalubale.(Saminu)