Wannan shi ne muhimmin sakon da wani rahoto kan karfin Afrika na shekarar 2015 na gidauniyar Afrika domin gina karfin ci gaba (ACBF), wata kungiya mai zaman kanta dake tallafawa dabarun gina karfin samun ci gaba a nahiyar Afrika, ta gabatar a ranar Litinin a birnin Harare.
Wannan rahoto ya kasance babbar gabatarwa ta ACBF, da ake fitar a ko wace shekara tun daga shekarar 2011.
A cewar wannan rahoto, ya zama wajibi ga Afrika da ta tattara albarkatunta na cikin gida domin cimma muhimman madarun ci gaba na karko na gabanin shekarar 2015, da kuma na ajandar shekarar 2063, da shirin tattalin arziki na Afrika.
Amma duk da haka, wannan ba yana nufin ba cewa, nahiyar ba za ta nemi albarkatu daga waje ba.
Amma ganin yadda tamaikon ci gaban jama'a yake raguwa a Afrika, ya zama wajibi ga nahiyar ta mayar da hankali kan tattara albarkatunta sosai na cikin gida domin samar hanyar bunkasa ci gaban ta, in ji wannan rahoto.
Sauran dalilan dake tilasta ganin Afrika ta tattara albarkatunta na cikin gida domin cimma burinta na bunkasuwa su ne cewa kasashen Afrika dake dogaro taimako suna kara nacewa wajen amincewa da bukatun masu ba su taimako fiye da mai da hankali kan muhimman bukatun cikin gida na jama'a, yayin da kuma kwararar kudaden waje take iyar zama babu tabbas.
A albarkacin fitowar wannan rahoto, ministan kudin Zimbabwe, Patrick Chinamasa, ya yi kiran kasashen Afrika da su kara karfafa karfinsu ta fuskar tattara albarkatun cikin gida, domin samar da kudaden gina hanyoyin ci gaba. (Maman Ada)