in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwarewar cigaban masana'antun Asiya, da ta Sin nada muhimmanci sosai ga nahiyar Afrika in ji darektan UNIDO
2015-12-13 14:01:35 cri

Nahiyar Afrika na samun damammaki ba kakkautawa ta fuskar cigaban masana'antu, da kwarewar da ta samu daga kasashen Asiya, musamman ma daga kasar Sin, nada muhimmanci sosai ga nahiyar, in ji mista Li Yong, darekta janar MMD game da cigaban masana'antu (UNIDO).

Mista Li yayi wannan furuci a ranar Laraba, a wata hirarsa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua.

A ranar Laraba da ta gabata, Tarayyar Afrika AU da UNIDO sun shirya wani dandali a birnin Geneva kan cigaban masana'antu da dorewa a Afrika.

Mista Li ya tunatar bayan taron cewa tun kama aikinsa shekaru biyu da suka gabata, UNIDO ta sanya cigaban masana'antu da dorewa a sahun gaban tsarinta.

UNIDO ta gamsu da ganin yadda dorewar masana'antu ya samu amincewa daga ajandar shekarar 2030 game da cigaba mai karko da aka amince da shi ba da jimawa ba da kuma maradun cigaba mai karko (SDGs), in ji mista Li.

Haka kuma ya jaddada cewa Afrika na samun damammaki ba kakkautawa ta fuskar cigaban masana'antu, ganin cewa salon tattalin arzikin nahiyar a wadannan shekaru 50 masu zuwa zai dogaro kan cigaban masana'antu.

Ajandar shekarar 2030 ta Afrika, da kungiyar AU ta cimma a farkon wannan shekara a matsayin wani shirin cigaba na tsawon lokaci, ya aza harsashin gaggauta cigaba da kuma bayyana yadda nahiyar take amfani da albarkatunta ta yadda al'ummarta mai tarin yawa, kusan biliyan daya za ta samu moriya.

Yana da kyau Afrika ta fara aiki da ajandarta don haka ta bukatar kasashen Asiya sosai, musammun ma kasar Sin, in ji mista Li. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China