in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin Afirka sun yaba wa shirye-shirye 10 na yin hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka
2015-12-06 13:07:49 cri

A yayin taron koli na Johanneburg na dandalin tattaunawar hadin gwiwa a tsakanin kasashen Sin da Afirka, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya sanar da daga matsayin huldar da ke tsakanin Sin da Afirka zuwa huldar abokantaka da hadin kai daga dukkan fannoni, tare da kaddamar da shirye-shirye guda 10 na yin hadin gwiwa a tsakanin sassan biyu. Jawabin Xi ya samu amincewa daga shugabannin kasashen Afirka.

Hage Gottfried Geingob, shugaban kasar Namibiya ya ce, wadannan shirye-shirye 10 za su biya bukatun Afirka sosai kuma cikin lokaci. Kamar yadda shugaba Robert Mugabe na Zimbabwe ya fada, kasar Sin ba ta taba yin mulkin mallaka a nahiyar Afirka ba, amma ta yi abubuwan alheri da ya kamata 'yan mulkin mallaka su yi.

Shugaba Thomas Boni Yayi na kasar Benin ya ce, shirye-shiryen 10 da shugaba Xi ya sanar sun dace da ajandar ayyukan raya Afirka na shekarar 2063 sosai, tabbas ne za su kara azama kan wadatuwar Afirka da ci gabanta.

Har wa yau Mokgweetsi Masisi, mataimakin shugaban kasar Botswana ya ce, jawabin Xi ya zo daidai da lokaci. Kasarsa za ta dauki wasu matakai, wadanda za su dace da shirye-shiryen 10, a kokarin cin gajiyarsu. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China