A yayin da aka gudanar da taron koli na Johanneburg na dandalin tattaunawar hadin gwiwa a tsakanin kasashen Sin da Afirka, Margaret Chen, babbar darektar hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO ta halarci wani taron yin rigakafin cutar AIDS cikin hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka a birnin, inda a cewarta, shirye-shiryen hada kan Sin da Afirka za su taimaka wajen kyautata yanayin kasashen Afirka na ba da magani da kiwon lafiya.
Madam Chen ta ce, a yayin taron kolin, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya sake jaddada kasancewar harsashi mai inganci a tsakanin Sin da Afirka ta fuskar yin hadin gwiwa, tare da sanar da shirye-shirye guda 10 na yin hadin gwiwa a tsakaninsu cikin shekaru 3 masu zuwa, ciki har da taimakawa kasashen Afirka wajen kyautata yanayin ba da magani da tsarin kiwon lafiya. Hukumarmu ta WHO ta yaba wa hakan. (Tasallah Yuan)