Jaridar People Daily ta kasar Sin ta ba da sharhi yau Lahadi 6 ga wata, mai taken "bude sabon shafi cikin hadin gwiwar kasashen Sin da Afirka, a kokarin samun ci gaba tare".
Sharhin ya ce, gudanar da taron koli na Johannesburg na dandalin tattaunawar hadin gwiwa a tsakanin kasashen Sin da Afirka, ya dace da moriyar dukkan kasashen Afirka da Sin, sa'an nan ya cimma burinsu duka.
Taron koli na Johannesburg, taron koli ne na biyu a tarihin huldar da ke tsakanin kasashen Afirka da Sin, haka kuma karo na farko da aka gudanar da taron koli a nahiyar Afirka, wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen inganta hada kan Sin da Afirka da kuma tsara manufar raya huldar da ke tsakanin sassan biyu a nan gaba.
Taron kolin ya kara azama kan raya Sin da Afirka tare bisa manyan tsare-tsare, inganta hadin gwiwarsu, kyautata samun moriyar bai daya na Sin da Afirka, da karfafa hada kan kasashe masu tasowa.
Yanzu an fara raya huldar abokantaka da hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka daga dukkan fannoni. Kasar Sin na son hada kai da 'yan uwanta na Afirka wajen yin kokari tare a fannin bude sabon shafi cikin hadin gwiwa, a kokarin samun ci gaba tare. (Tasallah Yuan)