in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Yi ya bayyana sakamakon da aka samu a yayin taron kolin Johannesburg na dandalin FOCAC
2015-12-06 11:41:41 cri
Bayan an kammala taron kolin Johannesburg na dandalin tattaunawar hadin gwiwar kasar Sin da kasashen Afirka, wato FOCAC a ranar Asabar 5 ga wata, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi da takwararsa ta kasar Afirka ta Kudu Maite Nkoana Mashabane sun gana da manema labaru tare, inda ya bayyana muhimmin sakamakon da aka samu a yayin wannan taron koli.

Mr. Wang Yi ya bayyana cewa, ana iya ganin wannan muhimmin sakamako a fannoni hudu.

Da farko dai, an bayyana sabon tunanin yin hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, wato "kasashen Sin da Afirka su hada kansu su nemi ci gaba da cin moriyar juna tare". Sannan, shugabannin kasashen Afirka wadanda suka halarci wannan taron koli sun amince da shawarar da shugaba Xi Jinping ya gabatar ta daga huldar dake tsakanin kasashen Sin da Afirka zuwa huldar abokantaka ta hadin gwiwa daga dukkan fannoni bisa manyan tsare-tsare. Na uku shi ne, kokarin karfafa tushe a fannoni 5 dake da alaka da huldar dake tsakanin kasashen Sin da Afirka, wato yin zaman daidai wa daida da amincewa da juna kan siyasa da yin hadin gwiwa da neman nasara tare kan tattalin arziki da yin mu'amala da koyon juna kan al'adu da wayin kai, da taimakawa juna kan tsaron kai da kuma yin hadin gwiwa kan harkokin kasa da kasa. Bugu da kari, a yayin taron, an tabbatar da muhimman shirye-shiryen yin hadin gwiwa a fannoni 10 wadanda suke dacewa da bukatun neman ci gaba da kasashen Afirka suke da su, da za su amfana wa dukkan jama'ar kasashen Afirka, kuma suke dacewa da yanayin da ake ciki a duniya wajen neman ci gaba.

A dadin dadawa, Wang Yi ya jaddada cewa, lokacin da kasar Sin take hada kai da kasashen Afirka, tana tsayawa kan matsayin magance bayar da kowane irin sharadin siyasa, ba ta tsoma baki kan harkokin cikin gidan kasashen Afirka ba, kuma ba ta tilasta wa sauran kasashen yin abu da ba su so ba, balle yin alkawarin da ba ta iya cikawa ba. Bugu da kari, a lokacin da take fitar da shirin yin hadin gwiwa, ta kan tantance bukatun da kasashen Afirka suke da su wajen kyautata zaman rayuwar jama'a da daga karfinsu na kokarin neman samun ci gaba da kansu.

Bugu da kari, Wang Yi ya bayyana cewa, a ganin kasar Sin, bai kamata a tsoma baki kan harkokin cikin gidan kasashen Afirka ba, ya kamata a bi babbar ka'idar dake da alaka da dangantakar dake tsakanin kasa da kasa. Na biyu, kasar Sin na goyon bayan kasashen Afirka da su warware matsalolin da suke fuskanta bisa hanyoyi nasu. Na uku, kasar Sin tana tsammani ya kamata a warware takaddama cikin ruwan sanyi. Daga karshe dai, ya kamata ya kamata a dauki matakan dake shafar fannoni daban daban a lokacin da ake kokarin warware wata matsala.

Sannan Wang Yi ya ce, kasar Sin tana fatan za ta zama abokiyar hadin gwiwa ta kasashen Afirka a lokacin da suke raya masana'antu. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China