Kaza lika, a yayin taron, an zartas da sanarwar taron kolin Johannesburg na FOCAC da kuma shirin Johannesburg daga shekarar 2016 zuwa shekarar 2018 na FOCAC bisa jagorancin da shugaba Xi Jinping ya bayar, inda kuma ya ba da jawabin rufe taron.
A yayin da yake jawabin rufe taron, shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma ya bayyana cewa, yana godiya matuka ga babbar gudummawar shugaban kasar Sin Xi Jinping, har ma da bangarorin kasar Sin baki daya suka samar wajen gudanarwar taron koli na wannan karo, kana, shugabannin kasashen Afirka da suka halarci taron sun nuna himma da kwazo ta aniyarsu wajen zurfafa hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka, sa'an nan, ko shakka babu, ra'ayoyin da aka cimma kan batutuwa da dama a yayin taron za su ciyar da bunkasuwar dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka gaba. (Maryam)