Da yake magana a gaban manema labarai a ranar Asabar a birnin Johannesburg, inda ya halarci taron koli na dandalin Sin da Afrika karo na biyu, shugaba Kenyatta ya bayyana cewa 'yan fadi karya fadi wofi dake korafi ko da yaushe cewa manufar kasar Sin a nahiyar Afrika za ta iya kasancewa daidai da ta 'yan mulkin mallaka.
Wannan wani tunani ne karya na bayyana cewa kasar Sin na zuwa Afrika domin yin mulkin mallaka, in ji shugaba Kenyatta.
Dubin cewa kasar Sin wata sabuwar 'yar mulkin mallaka wani abu ne na ba da labarin karya kan ayyukan Beijing a nan Afrika. Ayyukan moriyar juna da ake gudanar sun kasance bisa tushen huldar dangantaka tsakanin Sin da Afrika, in ji shugaban Kenya.
Inda ya kara da cewa, kasar Kenya ta gudanar da manyan ayyuka a fannoni daban daban kamar ci gaban ababen more rayuwa da musanyar kwararru dalilin sakamakon dangantaka tare da kasar Sin.
Ba na tunanin wani abokin hulda dake taimaka maka wajen kawar da talauci da wasu matsaloli na ci gaba za a kira shi wani dan mulkin mallaka. Kasar tana nuna mana yadda za mu hadin gwiwa tare domin cimma muhimman ayyukan ci gaba, in ji shugaban Kenya.
Shigar Sin a nahiyar Afrika ta fi maida hankali kan bukatunmu ba wai tana tunani kan abubuwan da za ta samu gare mu ba, a cewar Uhuru Kenyatta. (Maman Ada)