in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya tashi daga birnin Johannesburg inda yake kan hanyar dawowa kasar Sin
2015-12-06 07:51:05 cri
A ran Asabar, 5 ga wata da dare, an kammala taron koli na Johannesburg na dandalin FOCAC, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya tashi daga birnin da kama hanyar dawowa kasar Sin.

Wannan ne karo na 7 da Xi Jinping ya kai ziyara a nahiyar Afirka, kuma karo na biyu da ya kai ziyara a nahiyar bayan ya hau karagar mulkin kasar Sin a shekarar 2013. Kafin ya fara kai ziyara a nahiyar Afirka, sai da ya isa birnin Paris na kasar Faransa a ran 29 ga watan Nuwamba domin halartar babban taron tinkarar sauyin yanayin duniya da aka bude a ran 30 ga watan Nuwamba, tare da bayar da wani muhimmin jawabi mai taken "Yin hadin gwiwa wajen kafa tsarin tinkarar sauyin yanayin duniya domin kokarin neman nasara tare". (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China