in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
COP21: Sakamakon makon farko na shawarwari ya aza wani tushe mai karfi domin tarukan ministoci
2015-12-06 11:16:25 cri
Shugaban tawagar kasar Sin Su Wei ya tabbatar a ranar Asabar a yayin wani taron manema labarai a Bourget, cewa sakamakon makon farko na shawarwari kan takardar shirin yarjejeniya na Paris ta aza tushe mai karfi na matakin tarukan ministoci na COP21 na yarjejeniyar koli ta MDD kan sauyin yanayi (CCNUCC) dake aiki yanzu.

Bayan shan ayyuka sosai tsakanin masu tattaunawa na kasashe 195 a tsawon mako guda, an kai ga cimma wani sabon shirin yarjejeniya kan yanayi dake kunshe da takardu 21 sannan kuma aka mika su a ranar Asabar kamar yadda shugabancin taron COP21 tsaida.

Ayyukan mako mai zuwa za su kasance masu wuya da nauyi. A sabuwar takardar, har yanzu akwai wasu batutuwan da aka kasa cimma jituwa wadanda kuma bangarori ya kamata su yi musanya da kara tuntubar juna domin cimma wata yarjejeniya cikin gajeren lokaci, in ji mista Su, tare da bayyana cewa alkawuran siyasa na shugabannin kasashe da gwamnatoci a yayin bude taron COP21 sun taimaka wajen samun cigaba game da shirin tattaunawa.

Tawagar kasar Sin ta halarci sosai shawarwari kan shirin yarjejeniya ta yanzu kuma ta dauki niyyar ba da gudunmmawa har zuwa ga cimma sakamako mai kyau a taron sauyin yanayi na Paris. Matsayin da kasar Sin take da shi a cikin shawarwari na da tasiri kuma a bayyane da sauran bangarorin da abin ya shafa suka amince da shi, in ji mista Su Wei.

Haha kuma, ya jaddada cewa wannan shi ne wasu shawarwari na huldar dangantaka kana kokarin kasar Sin ita kadai ba zai sa a cimma wani sakamako mai gamsarwa ba. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China