in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An fara tattaunawa gabanin taron sauyin yanayi na birnin Paris
2015-11-30 09:52:23 cri

Ministan harkokin wajen kasar Faransa Laurent Fabius ya bukaci masu tattaunawa game da taron sauyin yanayi na duniya da zai gudana a birnin Paris na kasar Faransa, da su yi kokarin ganin an cimma yarjejeniya a karshen taron.

Mr Fabius yana karin haske ne yayin da rukunin masu tsara daftarin karshe game da taron suka fara ganawa a jiya Lahadi, kwana guda kafin isowar shugabannin kasashen duniya inda za su kara nasu bayanan game da yarjejeniyar da ake fatan cimmawa a taron na Paris.

Wakilin kasar Sin a taron na Paris Su Wei ya ce, wakilan za su yi amfani da lokacin da suke da shi don ganin sun cimma matsayar da za ta kai ga amincewa da wata yarjejeniyar da za ta magance matsalar sauyin yanayi a hukumance kafin ranar 11 ga watan Disamba.

Kimanin jami'an kasashe 200 da batun taron sauyin yanayi na MDD ya shafa ne za su nazarci yarjejeniyar yayin taron da za a bude a yau Litinin, inda shugabanin kasashe da na gwamnatoci a kalla 150 za su gabatar da jawabai.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China