in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Madam Peng Liyuan ta halarci aikin yaki da cutar AIDS na Sin da Afirka
2015-12-05 19:14:13 cri

A yau da safe ne, a kasar Afirka ta kudu uwar gidan shugaban kasar Sin, madam Peng Liyuan ta halarci aikin yaki da cutar AIDS da aka shirya tsakanin Sin da kasashen Afirka mai taken "Sin da kasashen Afirka su hada kansu domin samun al'ummar da babu cutar AIDS" tare da yin jawabin. Hukumar kiwon lafiya da kayyade iyali ta Sin da kungiyar yaki da cutar AIDS ta matan shugabannin kasashen Afirka suka jagoranci ga wannan shiri.

Bikin ya samu halartar darektan gudanarwa na hukumar yaki da cutar AIDS ta MDD, Michel Sidibe, da babbar darektar kungiyar kiwon lafiya ta MDD, madam Margaret Chan da sauran jama'a.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China