in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Madam Zuma ta yaba jawabinda shugaban kasar Sin ya gabatar a taron FOCAC
2015-12-05 19:04:42 cri

Shugabar hukumar zartarwar kungiyar tarayyar kasashen Afrika AU Madam Nkosazana Dlamini-Zuma ta yaba da jawabin da Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar a bikin bude taron kolin dandanlin hadin gwiwa tsakanin kasashen Afrika da Sin wato FOCAC da ya gudana a birnin Johannesburg na kasar Afrika ta kudu.

A cikin jawabin sa, shugaban Xi Jinping ya zayyana matakan da za'a dauka na habaka hadin gwiwwa tsakanin bangarorin biyu a fannonin ciniki,ababen more rayuwa, harkokin kudi da zuba jari, kiwon lafiya da tsaro.

Madam Zuma ta ce, kasashen Afrika a shirye suke su yi hadin gwiwwa da kasar Sin domin inganta tattalin arziki da inganta rayuwar jama'a

Ta kara da cewa hadin gwiwwa da kasar Sin zai yi matukar taimakawa nahiyar Afrika wajen aiwatar da shirye-shiryensu na samar da ababen more rayuwa da suke burin samarwa al'ummar su.

Madam Dlamini-Zuma daga nan sai ta gode wa shugaba Xi Jinping dangane da sanar da sabon shirin taimakon kudi ga kasashen na Afrika ta yadda za su cimma burin su na samar da ababen more rayuwa. Haka kuma ta yaba matuka akan bayanin da shugaban na kasar Sin yayi na cewar, al'ummar Afirka su magance matsalolinsu da kansu.

Shugabar hukumar gudanarwar ta AU har ila yau ta jaddada cewa akwai bukatar a baiwa nahiyar damar da zata inganta makomarta da kanta.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China