Erastus Mwencha, Mataimakin Shugaban na kwamitin kungiyar hada kan kasashen Afrika AU yace shugaba Xi ya gabatar da jawabi mai cike da ma'ana da kuma dama.
A lokacin hirar da ya yi da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, Mr Mwencha yace jawabin na shugaban kasar Sin a wajen taron na FOCAC ya yi ma'ana sosai yadda ya bayyana wani sabon fata na hadin kan bangarorin biyu.
Kasar Sin ta samar da kudade ga kungiyar AU domin taimaka mata aiwatar da jerin ayyuka da zai inganta cigaban al'umma.
Mr Mwencha ya jinjina ma shugaban kasar na Sin game da sanar da bayar da karin wassu kudade don taimaka ma cigaban tattalin arziki da inganta walwalan jama'a a Afrika.
Ita ma a nata bangaren Edna Molewa, Ministar sha'anin muhalli ta kasar Afrika ta kudu tace shugaban Xi ya shiga tunanin al'ummar Afrika kwarai lokacin da ya ke gabatar da jawabin sa a taron na FOCAC. Ta kara da cewa kasashen Afrika suna da imanin cewa Sin zata cika alkawarin ta na basu gudunmuwa a bangaren cigaban masana'antu, kare muhalli da kuma samar da ayyukan yi a nahiyar.
Shi kuwa Jakadan kasar Botswana a kasar Sin Sasara Chasala George cewa yayi shugabanin kasar Sin gaba daya suna goyon bayan kasashen Afrika wajen ganin sun cimma cigaba lami lafiya.
Ministan masana'antu da ciniki na kasar Zimbabwe kuwa, Mike Bimha ya shaida ma Xinhua cewa jawabin shugaban kasar na Sin ya bada kwarin gwiwwa sosai kuma ya jaddada zahirin manufar kasar game da dangantakar ta da kasashen Afrika.