in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen duniya sun nuna babban yabo kan kokarin Sin na tinkarar batun sauyawar yanayi
2015-11-29 14:14:10 cri
A kwanan baya, yayin da take magana da wakilin kamfanin dillancin labaru na Xinhua, shugabar shirin yanayi da makamashi na duniya na asusun halittun duniya (WWF), madam Samantha Smith ta bayyana cewa, kamata ya yi a nuna babban yabo kan kokarin da Sin ta ke yi a fannin tinkarar batun sauyawar yanayi. A jiya Asabar 28 ga wata, ministan harkokin waje na Faransa, Laurent Fabius ya furta cewa, matakan da Sin take dauka sun ba da gudummawa sosai wajen cimma matsaya daya kan shirin yanayin duniya da za a yi a birnin Paris.

Za a gudanar da babban taron sauyawar yanayi na Paris daga ranar 30 ga watan Nuwamba zuwa ranar 11 ga watan Disamban bana, inda madam Smith za ta halarci taron a matsayin wakiliyar wannan kungiya mai zaman kanta.

Madam Smith ta nuna amincewa da matakin da Sin take dauka na kayyade fitar da gurbatacciyar iska, da ka'idarta na daukar alhakinta a duniya amma kuma da banbanci a tsakaninta da sauran kasashe. Ta ce, ko da yake kasar Sin kasa ce mai tasowa, amma ta yi alkawari sosai a fannin tinkarar sauyawar yanayi, kuma ta sanar da kebe kudi yuan biliyan 20 wajen kafa asusun hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa domin tinkarar sauyawar yanayi.

Sai kuma a jiya Asabar, ministan harkokin waje na Faransa, kana shugaban taron sauyawar yanayi na Paris, Laurent Fabius ya bayyana cewa, matakan da Sin take dauka sun ba da gudummawa sosai wajen cimma matsaya daya tsakanin bangarori daban daban kan shirin yanayin duniya da za a yi a birnin Paris.

Mista Fabius ya kara da cewa, ya taba kai ziyara a Sin har sau 11 bayan da ya hau kujerar ministan harkokin waje na Faransa. A yayin ziyararsa a Sin kuma, ya gano da kansa cewa, Sin tana daukar hakikanin matakan tinkarar sauyawar yanayi.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China