in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon: Sin na taka muhimmiyar rawa wajen tinkarar sauyawar yanayi
2015-11-29 17:41:43 cri
Babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya bayyana cewa, Sin na taka muhimmiyar rawa wajen tinkarar sauyin yanayi.

Ban Ki-moon ya fadi haka ne gabanin babban taron tinkarar sauyawar yanayi da za a kira a ranar 30 ga wata a birnin Paris, inda ya ce, a shawarwarin da aka yi domin cimma matsaya daya a gun babban taron, Sin ta rika taka muhimmiyar rawa, kuma ya yi imani cewa, Sin za ta ci gaba da ba da gudummawa a wannan taro na Paris.

A sa'i daya, magatakardan MDD ya nuna babban yabo ga hadaddiyar sanarwar tinkarar sauyin yanayi tsakanin shugabannin Sin da na Amurka da aka fitar a watan Satumban bana, da hadaddiyar sanarwar tinkarar sauyawar yanayi tsakanin shugabannin Sin da na Faransa da aka fitar a watan Nuwamban bana, inda ya furta cewa, hadaddiyar sanarwar tsakanin shugabannin Sin da na Amurka wata alama ce da ta nuna cewa, kasashen biyu da suke da karfin tattalin arziki mafi girma a duniya suna da ra'ayi iri daya a fannin kayyade fitar da gurbatacciyar iska a nan gaba, yayin da hadaddiyar sanarwar tsakanin shugabannin Sin da na Faransa ta daidaita wasu manyan matsaloli, tare da ba da gudummawa sosai wajen cimma matsaya daya kan shirin tinkarar sauyin yanayi da za a daddale a birnin Paris.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China